Ci gaba daga makon da ya gabata
Wuri Na 6
Wuri na shida dake da matakan tsaro na musamman a Duniya shi ne wani wurin ajiye motoci da ke Kasar Ingila wanda ake kira da “Bold Lane Car Park”.
Wannan wuri yana daya daga cikin wuraren da ke da tsaro na musamman a Duniya, idan ka ajiye motarka a wannan wuri ba ruwanka da tunanin barayin mota, wasu daga cikin matakan tsaro da ke a wannan wurin ajiye mota sun hada da, idan ka zo ajiye mota sai an baka wani tikiti da ke dauke da wasu lambobin sirri (barcode) na tsaro wanda wurin da ka ajiye motar ne kadai ke da wannan lambobin sirri, kuma akwai wata na’ura mai gane motsin mota, da kuma karaurawar ko ta kwana, idan da za’ayi rashin sa’a wani ya dauki motarka to duka ginin wurin ajiye motar zai kulle gaba dayahar sai an warware matsalar.
- Ruhin Hanyar Ruwa Ta Red Flag Zai Ci Gaba Da Kasancewa Har Abada
- Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Ake Fama Da Karancin Mai A Abuja – IPMAN
Wuri na bakwai da ke da tsaro namusamman a Duniya shi ne wurin ajiyar kayayyaki na musamman da ake kira da “Iron Mountain”.
Shi wannan wuri yana boye ne a karkashin kasa, nisan kafa dari biyu, kuma akwai kofofi daban-daban wanda za su iya jure harin makamin kare dangi na nokiliya, kasashen Duniya da manya manyan kamfanunnuka suna kai takardunsu masu muhimmanci da ma bayanan sirrinsu domin wannan wuri ya ajiye musu, irin binciken da ake wa mutum kamin ya shiga wannan wuri, idan ma yana da wata ajiya a wurin kenan, sai ya kosa, domin komai da kake tare da shi sai an duba shi, haka kuma mafi yawan mutane da kamfanonin da suka yi ajiya a wannan wuri ba’a bayyana sunayensu.
Wuri na takwas da ke da matsanancin tsaro a Duniya shi ne wurin da aka ajiye wasu irin abinci na ko ta kwana da ake kira “Doomsday Seed Bault”.
Shi wannan wuri an tsara shi ne akan ajiye iri na abinci kala-kala da tsammanin ko wata masifar yunwa ko ta wani abu za ta fada wa Duniya da za ta sa mutane su rasa abinci, ta wannan wuri, kamar yadda suka ce ya tanadi abincin da zai wadaci mutanen Duniya, yana da katanga mai kauri sosai, akwai wasu irin makullan tsaro da ke amfani da iska da aka yi amfani da su wajen kulle shi, haka kuma yana da wata na’ura da ke tantance motsin mutum, an gina wurin ya shiga cikin kasa, ya kuma ratsa ta cikin wani dutse, da dai sauran matakan tsaro na musamman, sun ce ko da za’a harba makamin kare dangi na nokiliya kai tsaye akan wannan wuri ba zai ko da gezau ba, kuma wurin ya wuce gwajin girgizar kasa mai maki 6.2, don haka sun cika baki akan wannan wuri da yawa, sun ce babu abin da zai lalata shi.
Wuri na tara da ke da tsaro na musammana Duniya shi ne wurin ajiyar gwal na bankin Amurka “Federal Reserbe Bault”.
Wannan wuri an gina shi kafa tamanin karkashin kasa, kuma yana da wani bututu ko kuma a ce ma’ajiya wadda ita ta rufe bakin shiga wurin me nauyin da ya wuce tunani, mutum mutumi ake amfani da shi wajen shigar da gwalagwalan da ake ajiye wa a wurin, kuma akwai kwararrun maharba bindiga na gaske da aka ajiye suna jiran ko ta kwana, Amurka ta ajiye gwal a wannan wuri fiye da wanda ta ajiye a Fort Knod, haka kuma kasashen Duniya da da ma su ma suna jiye gwalagwalansu da yawa a wannan wuri saboda yarda da tsaron da ke wurin.
Bayan wadannan gurare da akwai kuma wasu gurare da ke da matsanantan tsaro kamar su. Wurin ajiyar gwal na Dubai.
Wurin ajiyar gwal na Kasar Swizerland. Maboyar tsohon Shugaban Kasar Iraki, Marigayi, Saddam Hussain, an gina ta yadda ko da bam din nukiliya ba zai yi mata illa ba, Kasar Amurka ta yi ta jefa bama-bamai a wurin lokacin da take so ta kama shi amma wurin bai lalace ba, sai da dabara sannan suka samu shiga wurin.
Wurin ajiyar gwal na Kasar Iran, shi ma wannan ba ma a san inda ma’ajiyar take ba, saboda barazanar takunkumi da Kasar Amurka ke mata.
Akwai wani wuri shi ma a Kasar Brazil da ake kira da tsibirin macizai, shi ma an hana zuwa wurin saboda a kare jinsin macizan daga karewa a doron Duniya.