Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta kasa, Baba Othman Ngelzarma ya bayyana yadda daukacin ‘yan kungiyar na kasa suka yi murna a kan matakin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na ba gwamnoni umarni su samar wa da Fulani makiyaya filayen kiwon shanunsu.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin taron manema labarai a dakin taro na gidauniyar Isa Yuguda ranar Asabar ta makon da ya gabata.
- Sin Ta Bayyana Adawa Da Zargin Blinken Wai Sin Na Gurbata Yanayin Sadarwar Duniya
- Finidi George Ne Zai Jagoranci Wasan Sada Zumunta Na Nijeriya Da Kasar Mali
Ya ce a cikin matakan su da suka dauka sun hada da kungiyoyin Fulani ba su goyon bayan ta’addanci, garkuwa da jama’a, satar shanu da sauran laifuka.
Ya akwai batun kar a kashe hukumar kula da ilimin ‘ya’yan makiyaya da ke karkashin ma’aikatar ilimi, gwamnonin da suke kafa kungiyarsa kai ta kare jiha su rika sa Fulani ciki kamar, kamar yadda Jihar Oyo ta yi, wanda ta kira da Fulani su sa ‘ya’yansu makarantar Boko. A cewarsa, suna bukatar gwamnati ta dauki mataki ba ya tsaya a rubuce ba.