Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi alkawarin kasar Sin ta shirya hada hannu da Poland wajen ingiza dangantakar da ke tsakaninsu zuwa sabon matsayi da kara tabbaci da daidaito a duniya mai cike da sarkakiya.
Xi Jinping ya bayyana haka ne jiya Litinin a Beijing, lokacin da yake tattaunawa da takwaransa na Poland Andrzej Duda, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.
Shi ma firaministan Sin Li Qiang, ya gana da shugaba Andrzej Duda a jiyan, inda ya bayyana kudurin Sin na inganta tsara manufofin samun ci gaba tare da Poland. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)