A yai ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron ilmi karo na 16 da taron manyan masana na cibiyoyin kimiyya na kasashe masu tasowa karo na 30.
A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, Sin na dora muhimmanci matuka kan bunkasuwar ilimin kimiyya, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya ciki hadda kasashe masu tasowa, don kara bude kofa da amince da juna da hadin kai tsakanin kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha, ta yadda zai amfani daukacin Bil Adam. (Amina Xu)