Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kananan hukumomin lardin Shanxi, tare da gabatar da wasu bukatu na ayyuka na mataki na gaba na wurin.
Xi ya ce, gina wani yankin gwaji na gyare-gyare na kasa, domin kawo sauyi kan tattalin arziki bisa albarkatun kasar, wani muhimmin aiki ne da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ya dorawa lardin Shanxi, don haka ya kamata a mai da hankali kan sauyin makamashi, da habaka masana’antu, da kuma samu ci gaba da ya dace.
Bugu da kari, Xi ya jaddada cewa, dole ne a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali yayin kawo sauyin ci gaba. Dole ne mu mai da hankali kan daidaita ayyukan yi, masana’antu, kasuwanni, da abubuwan da ake fata, da karfafa muhimman ayyukan kiyaye rayuwar jama’a kamar “tsofaffi da yara”, da tabbatar da rayuwar yau da kullum na mutanen da ba su da arziki.(Safiyah Ma)












