Kasar Sin ta samu babban sakamako a fannonin harba kumbuna masu dauke da mutane, da fannin sadarwar tauraron bil Adama, da fasahar kera roka da sauransu, bayan babban taron wakilan JKS karo na 18 da aka kira a shekarar 2012. Duk wadannan suna da nasaba da jagorancin babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping.
Binciken sararin samaniya buri ne na daukacin bil Adam, kuma shugaba Xi ya taba nuna cewa, kasar Sin tana nacewa kan manufar rayawa, da amfana daga albarkatun sararin samaniya, da hanyar da ta dace a ko da yaushe.
Ranar 24 ga watan Afirilun bana, ranar zirga-zirgar sararin samaniya karo na takwas ta kasar Sin ce, kuma kasar Sin tana gudanar da sabbin ayyukan da suka hada da binciken duniyar wata a mataki na hudu, da kara amfani da cibiyar sararin samaniyar ta da sauransu. Kuma a nan gaba, za ta kara azama, a fannin na nazarin sararin samaniya. (Mai fassarawa: Jamila)