• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Da Putin Sun Amince Su Zurfafa Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

by CMG Hausa
3 years ago
Xi

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a fadar Kremlin dake birnin Moscow jiya Talata, inda suka yi tattaunawa ta gaskiya, sada zumunci mai fa’ida kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da suka shafi moriyar juna.

  • Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Dawo Da Taimakon Kudin Da Ake Baiwa Sudan Ba Tare Da Wani Sharadi Ba

 

Sun kuma cimma sabbin fahimtar juna masu muhimmanci a fannoni da dama.
Bangarorin biyu sun amince da martaba ka’idojin makwabtaka, da abokantaka da hadin gwiwa tare da samun nasara wajen ciyar da mu’amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani.

Xi da Putin sun yi imanin cewa, mu’amalar da ke tsakanin bangarorin biyu a yayin ziyarar, tana da zurfi, mai kuma cike da wadata, ta kuma sanya wani sabon kuzari ga ci gaban hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani.

Bayan shawarwarin, shugabannin biyu sun rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin da tarayyar Rasha, kan zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani da kuma sanarwar hadin gwiwa na shugaban kasar Sin da na shugaban Tarayyar Rasha, kan shirin raya kasa nan da shekarar 2030 kan abubuwan da suka sanya a gaba a hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Rasha.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

A yayin ziyarar, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da dazuka, da binciken kimiyya da fasaha, da ka’idojin kasuwanci, da kafofin watsa labarai.
Da safiyar Larabar nan ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi zuwa kasar Sin, bayan kammala ziyarar aiki da ya kai kasar Rasha.

Kafin tashin Xi, mataimakin firaministan kasar Rasha Dmitry Chernyshenko, da wasu manyan jami’an Rasha sun shirya masa kasaitaccen bikin ban kwana a filin jirgin sama. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
NIS

NIS Reshen Ribas Ta Kafa Kwamitin Bunkasa Walwalar Jami’ai

LABARAI MASU NASABA

gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Xi

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.