A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana tare da manema labarai bayan tattaunawa a fadar Kremlin dake birnin Moscow. Inda Xi ya jaddada cewa, a yayin da yanayin kasa da kasa ke fuskantar sauye-sauye da hargitsi, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su yi riko da ruhin kyakkyawar makwaftaka kuma na dindindin, da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da hadin gwiwar samun moriyar juna da nasara tare, da habaka girma, fadi da juriyar dangantakar Sin da Rasha daga dukkan fannoni, da sanya karin kwanciyar hankali ga zaman lafiya da tsaro a duniya, da samar da kuzari ga ci gaban duniya da wadata. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp