Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Botswana Duma Boko, a yau Litinin, sun yi musayar taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Xi ya bayyana cewa, cikin shekaru 50 da suka gabata, tun bayan kulla huldar diflomasiyya, duk sauyin da yanayin duniya ya fuskanta, dangantakar Sin da Botswana ta ci gaba da samun ci gaba mai inganci, kasashen biyu sun zama aminai na kwarai masu daidaita juna a kan matsayi daya, da kuma abokan hadin gwiwa don samun ci gaba tare.
- ‘Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Mota A Kano
- Dalilin Da Ya Sa Legas, Abuja, Kaduna Suka Samu Masu Zuba Hannun Jari A Zango Na Uku
Xi ya kara da cewa, “A wannan sabon zamani, a shirye nake in yi aiki tare da shugaba Boko don kara inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, da tabbatar da goyon bayan manyan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, tare da ciyar da manufar kasashen biyu ta zamanantar da kai gaba, da bude wani sabon babi na dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Botswana.”
Boko a nasa bangaren kuwa, cewa ya yi Botswana ta samu kwarin gwiwa matuka sakamakon manyan nasarorin da kasar Sin ta samu, kuma tana fatan kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa tushen amincewa da mutunta juna, da yin aiki tare don aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka don samun ci gaba da wadata tare. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)