Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Singapore Tharman Shanmugaratnam sun taya juna murnar cika shekaru 35 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Xi ya bayyana cewa, huldar da ke tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da samun kyautatuwa tare da yin hadin gwiwa a fannoni daban daban da ke samar da sakamako mai inganci, ya kuma kara da cewa, bangarorin biyu sun samu ci gaba kafada da kafada a ayyukansu na zamanantarwa, inda hakan ya samar da ci gaba na zahiri ga jama’ar kasashen biyu.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana son zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a matakin koli, da karfafa cudanya a tsakanin jama’a, da kiyaye tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da muhimman ka’idojin da suka shafi dangantakar kasa da kasa.
A nasa bangaren, Shanmugaratnam ya bayyana cewa, bisa la’akari da bukatun zamani, bangarorin biyu sun kara fadada hadin gwiwa a wasu sabbin fannoni, yayin da al’ummomin kasashen biyu ke kara karfafa mu’amalar al’adu, kana ya ce, yana da cikakken imanin cewa, kasashen biyu za su ci gaba da yin aiki kafada da kafada da juna, tare da ciyar da dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon babban matsayi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp