Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taro na 23 na majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice, da maraicen yau Talata 4 ga wata a Beijing, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.
A jawabin nasa, Xi ya nuna cewa, a halin yanzu duniyar mu tana fuskantar rikice-rikice da yawa, kana, dan Adam na fuskantar kalubalen da ba’a taba ganin irinsa ba.
Tambaya a nan ita ce, hadin-gwiwa ko rarrabuwar kawuna, zaman lafiya ko rikice-rikice, zaman tsintsiya madaurinki daya ko zaman fito-na-fito, wane ake bukata? Amsa ta ita ce, fatan al’ummun kasa da kasa game da more rayuwa mai dadi, shi ne babban aikin dake gaban mu, kana kuma, babu wani mutum ko wata kasa, da za ta iya hana ayyukan wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba, da inganta hadin-gwiwa, da neman cimma moriya tare a duniyar mu.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kasar sa na fatan yin kokari tare da bangarori daban-daban, don aiwatar da shawarar tabbatar da tsaro a duk fadin duniya, da daidaita sabani tsakanin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari, da taimakawa wajen warware matsalolin kasa da kasa da na shiyya-shiyya ta hanyar siyasa.
Kaza lika kasar Sin tana kuma fatan yin kokari tare da bangarori daban-daban, wajen tabbatar da shawarar samar da ci gaban duk duniya, da tsayawa kan kokarin dunkule tattalin arzikin duniya na bai daya, da nuna adawa ga ra’ayin bada kariya, da sanya takunkumi a gefe daya, da ra’ayin nuna wariya da rarrabuwar kawuna, a wani kokari na kara samun nasarori don su amfani al’ummun kowace kasa bisa adalci. Kasar Sin tana maraba da bangarori daban-daban, da su aiwatar da shawarar inganta wayewar kai a duk fadin duniya, da nuna hakuri ga mabambantan al’adu, don kara samun fahimtar juna, da sada zumunta tsakanin jama’ar kasashe daban-daban.
A bana ne ake cika shekaru 10, tun bayan da kasar Sin ta bullo da shawarar “ziri daya da hanya daya”, inda za ta gudanar da babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3. Game da hakan, shugaba Xi ya ce, yana maraba da halartar bangarori daban-daban dandalin, ta yadda shawarar za ta kara samar da alfanu ga jama’ar duk fadin duniya. (Murtala Zhang)