A yammacin jiya ne, babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, wanda ya kai ziyarar gani da ido a birnin Guangzhou, hedkwatar lardin Guangdong dake kudancin kasar, ya je cibiyar bincike ta GAC, inda ya yi mu’amalar sada zumunta da masu bincike, da ’yan kasuwa, da ma’aikata, da wakilan masana’antun da ke samun tallafi daga kasashen ketare da sauransu.
Xi ya yi nuni da cewa, akwai bambanci matuka tsakanin hanyar da kasar Sin take bi wajen zamanantar da kanta da na kasashen yamma. Ya ce, ba za mu bi hanyar rarraba kawuna da wargaza wasu kasashe da kasashen yamma suka bi wajen zamanantarwa ba. Hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin, ta dogara ne kan hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki, ta kuma dace da yanayin kasar, tana da manufa, da tsare-tsare da dabaru, kuma za mu ci gaba da aiwatarwa bisa mataki-mataki. (Ibrahim Yaya)