Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aikin da kwamitin jam’iyyar Kwaminis ta Sin na jihar Xinjiang da gwamnatin jihar suka bayar, ya jaddada cewa, ya zama wajibi a aiwatar da cikakken tsarin tafiyar da harkokin jihar Xinjiang a sabon zamani a dukkan fannoni, da yin amfani da matsayin jihar Xinjiang bisa manyan tsare-tsare na kasar, don raya jihar mai hadin kai da jituwa da wadata da al’adu da jin dadin zaman rayuwa da kiyaye muhalli yayin da ake kokarin zamanintar da kasar.
A yau ne, bayan da shugaba Xi ya dawo kasar Sin bayan halartar taron kolin BRICS karo na 15, da ziyarar aiki a kasar Afirka ta Kudu, ya saurari wannan rahoton aikin a birnin Urumqi dake jihar ta Xinjiang. (Zainab)