A yau ne, shugaba Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga babban taron dandalin tattaunawa kan harkokin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa.
A cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, harkokin tafiyar da kare hakkin dan Adam na fuskantar kalubale. Muna son kare hakkin bil Adama ta hanyar kare tsaronsu, da girmama ’yancin kan kasashen duniya, da neman ci gaba cikin lumana, da kuma aiwatar da shawarar kare tsaron kasa da kasa, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau a fannin kiyaye hakkin bil Adama.
Haka kuma, ya ce, ana fatan inganta harkokin kare hakkin bil Adama ta hanyar neman bunkasuwa, a kokarin samun dauwamammen ci gaba cikin yanayi na adalci, ta yadda za a kare hakkin bil Adama yadda ya kamata ta hanyar zamanintar da kasa da kasa.
Bugu da kari, ya ce, akwai bukatar karfafa hadin gwiwa, da girmama juna, da shimfida yanayin adalci a yayin da ake inganta aikin kare hakkin bil Adama, da kuma aiwatar da shawarar wayewar kai ta kasa da kasa, da karfafa mu’amalar bangarori daban daban a wannan fanni, domin cimma matsayi daya kan yadda za a raya aikin kare hakkin bil Adama.
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da hukumar bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ne suka dauki nauyin shirya babban taron dandalin tattaunawa kan harkokin kare hakkin bil’adama na duniya.
Taken taron shi ne “Daidaita, hadin gwiwa, da samun ci gaba: bikin cika shekaru 30 da gabatar da sanarwar Vienna da shirin ayyuka da gudanar da hakkin dan-Adam na kasa da kasa”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)