An bude taron koli na farko kan raya al’adu a birnin Shenzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin da yammacin yau, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna.
Ya bayyana a cikin wasikar tasa cewa, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kuduri aniyar samar da sabbin daukakar raya al’adu na gurguzu.
Yana mai cewa, wajibi ne a aiwatar da tunanin tsarin mulki na gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani daga dukkan fannoni, da sauke nauyin dake wuyanmu don raya al’adu da kara yarda da al’adunmu da bude kofa da amincewa da sauran al’adu da ma nacewa ga yin kirkire-kikire tare, ta yadda za a karawa al’umma kwarin gwiwar yin kirkire-kirkire kan al’adun al’umma, da wadatar da al’adu bisa tushen tarihi da kafa kasa dake da al’adu mai karfi da ingiza mu’ammalar wayewar kan bil Adama tsakanin al’ummomi daban-daban. (Amina Xu)