Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da binciken ra’ayoyin jama’a masu amfani da shafukan Intanet kan aikin tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a kwanan nan, inda ya ce, ya kamata aikin tattara ra’ayoyin jama’a ta yanar gizo wajen tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ya samu shigar jama’a sosai, kuma ya kasance wani aiki na dimokuradiyya dake shafar dukkan bangarori.
Jama’a sun yi ta ba da shawarwari tare da gabatar da ra’ayoyi masu muhimmanci, wadanda ya kamata sassan da abin ya shafa su yi nazari a hankali tare da shigar da su cikin tsarin. Kuma dole ne kwamitocin JKS da gwamnatoci a dukkannin matakai su bi tsarin da ya shafi al’umma, su gudanar da bincike mai zurfi kan ra’ayoyin jama’a, da sauraron muryoyinsu, da shigar da hikimominsu cikin tsarin, ta yadda za a samar da hadin gwiwa mai karfi don ingnta zamanintarwa irin ta kasar Sin, da ci gaba da tabbatar da cikar burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa.
Daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa ranar 20 ga watan Yunin bana, an fara aikin tattara ra’ayoyin jama’a kan tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ta yanar gizo, kuma an bullo da shiri na musamman a shafin intanet na Jaridar People’s Daily, da na kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da shafin intanet na babban rukunin gidajen rediyo da talbijin na kasar Sin wato CMG, da kuma kan dandalin “Learning Power”, don neman ra’ayoyin jama’a.
Ya zuwa yanzu, aikin ya sami shawarwarin jama’a masu duba shafin intanet sama da miliyan 3, tare da samar da muhimman bayanai don tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp