Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da ayyukan bin doka a kowane fanni, inda ya bayyana cewa, tun bayan babban taro na 18 na jam’iyyar kwaminis ta Sin da aka kira a shekarar 2012, an samu ci gaba wajen kafa tsarin bin doka a kowane fanni, inda tsarin shari’a na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani ya kasance yana ta samun kyautatuwa da fadada.
Xi ya jaddada cewa, dole ne a aiwatar da tunanin shari’a na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani daga dukkan fannoni. Kazalika, a hade kiyaye jagorancin JKS, da barin jama’a su gudanar da harkokin kasa da bin doka waje guda, a kuma mayar da hankali kan gina cikakken irin wannan tsari na shari’a, da gina kasa mai ingantaccen tsarin shari’ar, da kara mai da hankali kan hadin gwiwar bangaren shari’a, da yin kwaskwarima a gida, da samun ci gaba, kana da samun kwanciyar hankali.
Bugu da kari, a kara zura ido kan tabbatar da adalci a cikin al’umma, da martaba doka sau da kafa cikin adalci tsakanin al’umma, ta yadda za a samar da ginshiki mai inganci a bangaren doka da shari’a, don samun ingantattun ci gaban kasa, da farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanintar da al’umma. (Amina Xu)














