A kwanan baya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi tsokaci kan aikin raya sabbin nau’ikan masana’antun kasarsa, inda ya ce aikin yana da matukar muhimmanci ga burin kasar Sin, na neman zamanantarwa da raya al’umma, saboda haka ana bukatar samun ci gaba, a fannin nazarin kimiyya da fasaha, da yin kwaskwarima kan tsare-tsaren masana’antu, ta yadda za a tabbatar da ingancin ayyuka a matakai daban daban, da aza harsashi ga aikin kasar na neman zamanantarwa ta wata dabarar kanta.
An gudanar da taron raya sabbin nau’ikan masana’antu daga jiya Juma’a zuwa yau Asabar, a birnin Beijing na kasar Sin, inda aka sanar da umarnin da shugaba Xi Jinping ya bayar. (Bello Wang)