Shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a rubuce mai taken “Yi amfani da yanayin zamani, da samar da wadata a duniya baki daya”, a gun taron kolin CEO na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya-Fasifik wato APEC da aka gudanar a Lima, hedkwatar Peru, a safiyar jiya Jumma’a bisa agogon wurin.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, dole ne a jagoranci dunkulewar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata, da yin aiki tare don inganta bude alakokin tattalin arzikin duniya, da daukaka dunkulewar tattalin arzikin duniya zuwa wani sabon mataki na kara kuzari, da hada kai, da dorewa, ta yadda za su amfanar da kasashe da al’ummomin duniya daban daban.
- Rikicin PDP: A Daina Maganar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2027, A Maida Hankali Kan Jam’iyya –Saraki
- An Kafa Kawancen Hadin Gwiwar Taron Masanan “Global South”
Shugaban ya ce, abu na farko, ya kamata a tsaya tsayin daka kan kirkire-kirkire don inganta ci gaban tattalin arzikin duniya mai karfi.
Na biyu shi ne dagewa wajen ci gaba da tafiya tare da zamani, da inganta yin kwaskwarima ga tsarin kula da tattalin arzikin duniya.
Na uku shi ne a dage wajen dora muhimmanci kan bukatar mutanen duniya, da inganta hanyoyin magance matsalar rashin daidaiton ci gaba.
Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata kasar Sin da sauran kasashen Asiya da Pasifik su karfafa hadin gwiwa don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskantar, da kuma hada karfi don sa kaimi ga bunkasar duniya, tare da samar da makoma mai kyau ga bil’adama.(Safiyah Ma)