Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan Hungary, Viktor Orban, yau Litinin a birnin Beijing.
Xi ya kuma taya Hungary murnar kama ragamar shugabancin karba-karba na Tarayyar Turai. Yana mai jaddada cewa, babu wata rigima ta siyasar duniya tsakanin Sin da Turai.
- Kasar Sin Na Tunawa Da Kutsen Japan Tare Da Nanata Muhimmancin Neman Ci Gaba Cikin Lumana
- Wani Kamfanin Kasar Sin Ya Kammala Aikin Shimfida Hanyar Mota A Kasar Comoros
A nasa bangare, Viktor Orban ya ce Hungary na goyon bayan karfafa dangantaka da Sin, kuma tana adawa da kafa kananan rukunoni da fito na fito tsakanin bangarori, haka kuma a shirye take ta yi amfani da shugabancinta na Tarayyar Turai a matsayin dama ta inganta dangantakar Sin da EU
Ya kuma yi karin bayani game da ziyararsa ta baya-bayan nan a Ukraine da Rasha.
Bugu da kari, shugaba Xi ya yaba da kokarin da Orban ke yi na samar da mafita a siyasance ga ricikicin Ukraine. Yana mai karin bayani game da shawarwari da ra’ayin Sin don gane da batun.
Shugaba Xi Jinping ya kara da nanata cewa, tsagaita bude wuta da wuri da ma dakatar da yaki, da neman mafita a siyasance, sun dace da muradun dukkan bangarori. Kuma Sin na nata kokari wajen inganta hawan teburin sulhu da karfafa gwiwa da mara baya ga dukkan kokarin da suka dace da warware rikicin cikin lumana. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)