Da safiyar yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da baki mahalarta taron sada zumunta tsakanin Sin da ketare, kana bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar sada zumunta tsakanin Sin da ketare a nan birnin Beijing.
Xi ya ce, Sin na fatan karfafa mu’amala da cudanya da kasashen duniya, tana mai fatan kafa kyakkyawar makomar Bil Adam ta bai daya cikin hadin gwiwa ta hanyar amfani da karfin al’umma na musamman a bangaren diplomasiyya.
- CBN Ya Sake Nanata Ba Da Kariya Ga Kudaden Ajiya A Bankuna
- Yunkurin Magance Matsalar Tsaro Da Rigingimu A Arewa…
Ya kamata a kai ga matsaya daya tsakanin al’umommi kan wannan muhimmin aiki, daga baya kuma a nace ga ra’ayin cin moriya bisa hadin gwiwa don gaggauta aikin zamanintar da duniya mai samun bunkasuwa cikin lumana da samun wadata tare. Kana da yin mu’amalar al’adu a maimakon jan kangiyar tsakanin mabambantan al’adu, da koyi da juna a bangaren al’adu a maimakon yin rigingimu a wannan bangare, bisa ra’ayin bude kofa da yin hakuri.
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo da tsohon shugaban majalisar gudanarwar Thailand Bhokin Bhalakula da dai sauransu sun halarci bikin tare da gabatar da jawabai. Sun ce, shawarar da Xi Jinping ya gabatar ciki har da kafa kyakkyawar makomar bai daya ga bil Adama da “ziri daya da hanya daya” da sauransu, sun bayyana basira da hangen nesa da ma nauyin dake wuyan kasar Sin wajen daidaita harkokin kasa da kasa. (Amina Xu)