Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella a yau Juma’a a nan birnin Beijing.
Xi ya bayyana cewa, bana ce ta cika shekaru 20 da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Italiya. Kana bangarorin biyu sun fitar da wani shiri na karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, tare da tabbatar da kiyaye ruhin hanyar siliki da ya jure lokaci, da ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki na ci gaba. A matsayinsu na kasashe biyu masu dadadden wayewar kai, ya kamata Sin da Italiya su ci gaba da raya al’adar bude kofa, da hada kai, da karfafa gwiwar al’ummomin kasa da kasa da su warware sabanin ra’ayi ta hanyar yin shawarwari, da kaucewa rigingimu ta hanyar hadin gwiwa, da yin aiki tare don gina kyakkyawar duniyar hadin gwiwa da zaman tare.
A wannan rana har ila yau, Xi da Mattarella sun gana tare da wakilan sassan biyu dake halartar taron tsarin hadin gwiwar al’adu na Sin da Italiya da kuma tattaunawa tsakanin shugabannin jami’o’in Sin da Italiya. Xi ya bayyana fatan cewa, bangarorin biyu za su yi aiki tare don karfafawa masu hangen nesa da dama gwiwa, don su zama masu yin hadin gwiwa a fannin sada zumunta tsakanin Sin da Italiya, masu sa kaimi ga fahimtar juna tsakanin wayewar kan gabashi da yammacin duniya, kuma masu shiga a dama da su wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama, ta yadda za a ba da gudummawar Sin da Italiya wajen sa kaimi ga samar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Yahaya)