Da safiyar yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Vietnam To Lam a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A halin yanzu, shugaba To Lam na kasar Vietnam yana ci gaba da gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin.
A yayin ganawarsu, Xi Jinping ya bayyana cewa, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Vietnam, Jam’iyyun Kwaminis ne biyu dake mulkin kasashensu, don haka ya kama jam’iyyun biyu su nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakaninsu, yayin da suke zurfafa aikin gina al’ummar Sin da Vietnam mai makoma ta bai daya bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za su inganta bunkasuwar manufar gurguzu ta kasashen duniya cikin hadin gwiwa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp