Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha yayin da suke halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO dake gudana a Astana, fadar mulkin Kazakhstan a daren jiya Laraba.
Xi Jinping ya ce, ya kamata Sin da Rasha su ci gaba da rike ka’idarsu don sada zumunci daga zamani zuwa zamani, da ma nacewa ga amfanawa al’umomminsu duk da sauye-sauyen da ake fuskanta a duniya. Tare kuma bullo da karfin hadin gwiwarsu daga zuciya, da kara taka rawa wajen kare muradun kasashen biyu da ka’idar huldar kasa da kasa. Sin na fatan ci gaba da hadin gwiwarta da Rasha da sauran mambobin kungiyar, don gaggauta bunkasuwar kungiyar da kafa kyakkyawar makomar bai daya ta kunigyar. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Rasha su ci gaba da hadin kai bisa tsarinsu a dukkanin fannoni, da adawa da shisshigi daga kasashen waje, da ma kiyaye kwanciyar hankali mai karko a wannan yanki.
A nasa bangare, Putin ya ce, a halin yanzu, huldar kasashen biyu ya kai matsayin koli a tarihi, bangarorin biyu na mutunta juna da cin moriya tare bisa daidaito, Rasha da Sin ba za su kafa karamin rukuni da nuna kiyayya ga saura ba, duk wadannan abubuwa sun dace da muradun jama’ar kasashen biyu. Rasha na goyon bayan kasar Sin da ta kare muradunta mai tushe da ikonta mai dacewa, da adawa da sauran kasashe ma su tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da batun tekun kudancin Sin. (Amina Xu)