Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan tawagar rukunin da suka yi aikin kera babban jirgin saman fasinja kirar C919 a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, kana ya halarci bikin nune-nunen nasarorin da aka cimma, inda ya yaba da nasarorin da aka samu game da aikin kera jirgin saman.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, shawagin babban jirgin sama kirar kasar Sin a sararin sama, shi ne burin kasa da al’ummar Sinawa da kuma jama’ar Sin. Ya ce ya kamata a yi amfani da fifikon sabon tsarin albarkatun kasar, da martaba ka’idojin tabbatar da tsaro da inganci daga farko zuwa karshe a kan aikin, da kara samun ci gaba kan muhimman fasahohi daga aikin, da kuma gaggauta raya wannan sha’ani da raya kasar mai karfin masana’antu.
Babban jirgin saman samfurin C919, shi ne jirgin sama na farko da kasar Sin ta kera da kanta bisa ma’aunin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, wanda ke da ikon mallakar fasaha mai zaman kansa.
An fara aikin nazarin kera jirgin saman ne a shekarar 2007, kuma jirgin ya yi gwajin tashi na farko a shekarar 2017, inda ya kammala dukkan bincike da samun takardar iznin yin zirga-zirga ta kasar Sin a watan Satumba na shekarar 2022. A karshen shekarar 2022 ne, jirgin zai fara shiga kasuwa. (Zainab)