Da maraicen yau Laraba 6 ga wata ne, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasa, kana shugaban kwamitin sojan tsakiyar kasar Xi Jinping, ya gana da wasu membobi daga bangarorin jam’iyyar Revolutionary Committee Of The Chinese Kuomintang, da na kimiyya da fasaha, da na muhalli da albarkatu, wadanda ke halartar zama na biyu na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar wato CPPCC karo na 14, tare da halartar taron tattaunawarsu, da jin ra’ayoyi gami da shawarwarinsu.
Yayin da bikin ranar mata na kasa da kasa ke gabatowa, wanda zai fado a ranar 8 ga watan da muke ciki, a madadin kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya yi barka da ranar mata da mika gaisuwar fatan alheri, ga mata daga kabilu da bangarori daban-daban na kasar Sin, gami da mata daga yankunan Hong Kong da Macau da na lardin Taiwan, da mata Sinawa dake zaune a kasashen ketare. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp