Da safiyar yau Juma’a 31 ga Oktoba, an yi kwarya-kwaryan taron zango na farko na shugabannin APEC karo na 32 a cibiyar taro dake birnin Gyeongju, bisa taken “Gina tattalin arzikin Asiya da Pasifik mai bude kofa da hada kowa”.
A cikin jawabinsa, Xi ya nuna cewa, tun bayan kafuwar APEC fiye da shekaru 30 da suka gabata, ta kasance tana jagorantar ci gaban yankin Asiya da Pasifik a fagen bude kasuwanci da ci gaba. Ya kara da cewa, a halin yanzu, yanayin duniya na samun sauye-sauye ciki sauri, yayin da yankin Asiya da Pasifik ke fuskantar karuwar rashin tabbas. Ya bukaci dukkan bangarorin da su ci gaba da more damammaki na ci gaban bude kasuwanci, su kuma inganta tattalin arzikin duniya mai hada kowa, da kuma gina al’ummar Asiya da Pasifik ta bai daya.
Shugaba Xi ya kuma gabatar da shawarwari guda 5. Na farko, kiyaye tsarin kasuwanci na mabambantan bangarori. Na biyu kuwa, samar da yanayin tattalin arziki na yanki mai bude kofa. Baya ga hakan, hada kai wajen kiyaye tabbaci da ingantaccen tsarin samar da kayayyaki. Na hudu, inganta kasuwancin fasahar zamani da kuma kare muhalli cikin hadin gwiwa. Na karshe, inganta ci gaban tattalin arziki mai hada kowa da kowa tare.
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)
 
			




 
							







