Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin JKS, ya jaddada bukatar mayar da hankali kan kokarin gina kasar zuwa mai karfin al’adu ya zuwa shekarar 2035.
Xi Jinping ya bayyana hakan ne yau Litinin yayin da yake jagorantar wani zaman nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS.
Ya kuma nanata bukatar ci gaba da raya al’adun gurguzu mai sigar kasar Sin a sabon zamani. (Fa’iza Mustapha)