Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa ta bai daya, tare da raya tattalin arziki na teku mai inganci da dai sauransu.
A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kafuwar babbar kasuwa ta bai daya a ciki kasar Sin ta dace da bukatunmu na bullo da sabon tsarin neman ci gaba da samun bunkasa mai inganci, don haka ya kamata a aiwatar da aikin bisa manufar kwamitin tsakiya, da daidaita ayyuka yadda ya kamata, domin cimma burinmu cikin hadin gwiwa.
Haka kuma, ya ce, ya kamata a inganta bunkasa tattalin arziki na teku kamar yadda ake bukata domin ciyar da zamanantarwar kasar Sin gaba, tare da neman hanyar raya kasa ta teku bisa yanayin da kasar Sin take ciki. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp