Yau Juma’a a birnin Beijing na kasar Sin, an yi taron karramawa fitattun mutane masu bukata ta musamman. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya taya fitattun kungiyoyi ko daidaikun mutane masu bukata ta musamman murnar samun lambobin yabo, albarkacin ranar taimakawa mutane masu bukata ta musamman karo na 35 ta kasar.
Shugaba Xi ya ce, mutane masu bukata ta musamman muhimmin karfi ne dake ingiza sha’anin zamanantar da al’ummun Sin, kuma suna bukatar samun kulawa daga daukacin al’ummun kasar. Ya ce, dole ne a nace ga matsayin jagorancin ra’ayin tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani, don raya cikakken tsarin rufawa mutane masu bukata ta musamma baya, da ba su kulawa mai kyau, ta yadda za a tabbatar da muradunsu, da ciyar da sha’anin dake da nasaba da su zuwa gaba a dukkan fannoni.
Xi ya kuma nanata kira ga kwamitocin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatoci a wurare daban-daban, da su dora muhimmanci matuka kan ayyukan kula da mutane masu bukata ta musamman, kuma a yi iyakacin kokarin samar da kyakkyawan yanayi a zaman al’umma, na fahimta da mutuntawa da ba da kulawa ga mutane masu bukata ta musamman. Yana fatan mutane masu bukata ta musamman za su yi koyi da wadanda aka ba lambobin yabo, wajen tinkarar mawuyacin hali, da kokarin daidaita matsalolin dake gabansu, da kuma cimma muradu da burinsu bisa himma da kwazo, ta yadda za su taka rawar gani wajen samun ingantacciyar bunkasuwar kasa da farfadowar al’ummun Sin bisa tsarin zamanantar da al’ummar kasar daga dukkan fannoni. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp