A yau Litinin, ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar da taro domin nazarin wani rahoto, na zagaye na 3 na rangadin tabbatar da da’a da kwamitin kolin karo na 20 ya kaddamar.
Sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping ne ya jagoranci taron.
- Xi Jinping Ya Jaddada Bukatar Gina Sin Zuwa Kasa Mai Karfin Al’adu Ya Zuwa 2035
- Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Samarwa Yankin Taiwan Makamai
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron, ta ruwaito sakamakon rangadin ya nuna cewa, an karfafa akidun jam’iyya a tsakanin shugabancin jam’iyyar da sassan gwamnati da cibiyoyin kudi na gwamnatin tsakiyar.
Taron ya yi kira da a shawo kan batutuwan da aka gano yayin rangadin domin daukaka samar da ci gaba mai inganci ta hanyar ingantacciyar gyara.
Har ila yau, taron ya nanata bukatar dorewar mataki mai tsauri da ake dauka kan cin hanci da rashawa. Ya kuma yi kira da a kawar da tushen abubuwan da ke bada damar aikata cin hanci da yaki da shi akai-akai kuma bisa hanya mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp