Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadi a lardin Guangdong. Da farko ya kai ziyara a birnin Zhanjiang, inda ya duba yadda ake gudanar da ayyuka noma a cibiya ta kudu ta kasar dake renon ire-iren amfanin gona da ruwan teku, da yankin gandun daji na itacen mangrove na tsibirin Jinniu, da tashar jiragen ruwa ta Xuwen, da aikin rarraba albarkatun ruwa ga wuraren dake kewayen tekun arewaci, da ma fahimtar halin da ake ciki game da kamun kifi da kiyaye gandun daji na itacen mangrove da inganta manyan ababen more rayuwa na sufuri, tare da ingiza hadin kan lardunan Guangdong da Hainan don samun bunkasuwa tare, da kyautata tsarin rarraba albarkatun ruwa a wurin da sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp