Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci Sin da Faransa su kasance karfi abun dogaro wajen tabbatar da odar duniya da inganta ci gaban duniya da jagorantar hadin kai tsakanin kasa da kasa.
Da yake zantawa ta wayar tarho da shugaba Emmanuel Macron a yau Alhamis, Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Faransa da su hada hannu wajen kare matsayi da ikon MDD da kare ka’idojin cinikayya na duniya da odar duniya da kuma tabbatar da cudanyar bangarori daban daban.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana daukar Turai a matsayin mai zaman kanta a duniyar dake da kasashe daban daban masu karfi. Ya ce, Sin na goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta karfafa cin gashin kanta da taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa. Har ila yau, ya ce, a shirye Sin take ta hada hannu da EU wajen shawo kan kalubalen da duniya ke fuskanta da cimma karin sakamakon da za su amfani bangarorin biyu da ma duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp