Da yammacin yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Benin Patrice Talon, wanda ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka sanar da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Xi Jinping ya nuna cewa, Sin na goyon bayan nahiyar Afrika, a fannin zama wani muhimmin bangare na siyasa, da tattalin arziki, da al’adu a duniya, tana kuma mai fatan samar da sabbin damammaki bisa ci gaban da take samu, da kuma hadin kai da kasashen Afirka ciki har da Benin, don tabbatar da ci gaban da aka samu, a dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, da ingiza shawarar “ziri daya da hanya daya”, da shawarar raya duniya ta bai daya, da ma ajandar 2063 ta AU, da kuma tabbatar da tsare-tsaren bunkasuwar kasashen Afrika, har ma da goyon bayan kasashen nahiyar wajen samun farfadowar tattalin arziki, da bunkasuwa mai dorewa.
A nasa bangare, Patrice Talon cewa ya yi, shugabannin biyu sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban, ciki har da zurfafa hadin kai wajen tabbatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da samun bunkasuwa, tare da kiyaye muhalli, da kayayyakin aikin gona, da kiwo lafiya da sauransu. Ban da wannan kuma, an gabatar da sanarwar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.
Sannan, a Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya takwaransa na kasar Zimbabwe Emmerson Dambudzo Mnangagwa, murnar zarcewa a mukamin shugaban kasa.
A sakon na sa ta wayar tarho, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, Sin da Zimbabwe na da hulda mai kyau. Kaza lika a shekarun baya-bayan nan, kasashen biyu na karfafa fahimtar juna a siyasance, tare da samun sakamako mai armashi a fannin hadin kai, da goyon bayan juna kan muradunsu masu tushe, a karkashin jagorancin shugabannin biyu.
Xi ya kara da cewa, Sin na dora muhimmanci matuka kan bunkasuwar huldar kasashen biyu, yana kuma mai fatan kara hadin kai da Emmerson Dambudzo Mnangagwa, a fannin ingiza samun sabon ci gaba, ta fuskar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye adalci da daidaito na kasa da kasa, da muradun bai daya na kasashe masu tasowa.
Bugu da kari, a yau Juma’a shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jajantawa takwaransa na kasar Afrika ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa, bisa gobara da ta tashi a wani gini dake birnin Johannesburg, wadda kuma ta haddasa rasuwar mutane da dama.
Xi Jinping ya ce, a madadin gwamnatin Sin da jama’arta, yana jajantawa iyayen mamatan da bala’in ya ritsa da su. Ya ce, Sin na goyon bayan gwamnatin Afrika ta kudu da jama’arta. Ya kuma yi imanin cewa, a karkashin jagorancin Ramaphosa da gwamnatinsa, ba shakka jama’ar kasar za ta shawo kan wannan bala’in. (Amina Xu)