Da yammacin yau Laraba 29 ga wata, a babban dakin taron al’umma dake Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar Sin.
Xi ya ce, a shekaru 68 da suka gabata, tsakanin kasashen Larabawa da na Afirka, Masar ce ta fara kulla huldar jakadanci tare da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, kuma dangantakar Sin da Masar ta zama wani kyakkyawan misali dake shaida hadin-gwiwa, da samun moriyar juna tare tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, da na Afirka, da na kasashen musulmi, har ma da kasashe masu tasowa.
- Peng Liyuan Ta Yi Zanta Da Mai Dakin Shugaban Kasar Equatorial Guinea
- Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Equatorial Guinea
Xi ya kuma jaddada cewa, kasarsa na fatan kara tuntubar juna, da karfafa hadin-gwiwa tare da Masar, da ma sauran bangarori daban-daban, don raya dandalin tattauna hadin-kan Sin da kasashen Larabawa, da sanya sabon kuzari ga ci gaban dangantakar kasashen biyu, gami da raya al’ummominsu masu kyakkyawar makoma ta bai daya.
Bangarorin biyu sun kuma yi musanyar ra’ayi, kan batun da ya shafi rikicin Palesdinu da Isra’ila.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu, sun gane ma idanunsu yadda aka rattaba hannu kan wasu takardun hadin-gwiwa, wadanda suka shafi shirin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin-gwiwa, da na kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da zuba jari, da hadin-gwiwar tattalin arziki, da binciken cututtuka masu yaduwa da sauransu.
Bangarorin biyu sun kuma fitar da hadaddiyar sanarwa, mai nasaba da zurfafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare, daga dukkanin fannoni tsakaninsu.
Kafin shawarwarin, shugaba Xi ya shirya wani biki a wajen babban dakin taron al’ummar, don maraba da zuwan shugaba Sisi.
Bisa goron gayyatar da shugaba Xi ya mika masa, shugaba Sisi na kasar Masar, na gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, inda kuma zai halarci bikin kaddamar da taron ministoci karo na 10, na dandalin tattauna hadin-kan kasar Sin da kasashen Larabawa. (Murtala Zhang)