Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sakon taya murnar budewar dandalin mata na kunigyar hadin kai ta Shanghai(SCO).
Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce, kasancewar mata masu ingiza ci gaban al’adu da al’ummar Bil Adama, suna taka muhimmiyar rawa ga ci gaban sana’o’i daban-daban. Sin na fatan hadin gwiwa da kasashe daban-daban wajen gaggauta bunkasuwar aikin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sha’anin mata ta amfani da fasahar yanar gizo ko Internet, ta yadda za a raya harkokin kungiyar SCO cikin hadin gwiwa.
An bude wannan dandali a birnin Qingdao na lardin Shandong na Sin a yau Laraba, mai taken “Fasahar yanar gizo dake karfafawa mata kwarewar aiki, da sanya mata su shiga a dama da su a ayyukan raya tattalin arziki”. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp