Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar kaddamar da jirgin ruwa mai aikin nazari a teku mai zurfi samfurin “Meng Xiang” wato “kyakkyawan fata”.
Kaddamar da wannan jirgin ya alamanta cewa, kasar Sin ta cimma muhimmiyar nasara a bangaren shiga da nazari da kuma raya teku mai zurfi, kuma babban ci gaba ne wajen zama kasa mai karfi a bangaren nazarin teku da kimiyya.
Shugaba Xi ya yi fatan za a yi amfani da wannan jirgi don gaggauta aikin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya, da fasahohin teku, da habaka hadin kan kasa da kasa kan nazarin teku, ta yadda za a taka karin rawar gani ga gaggauta zamanintar da al’ummar Sinawa, da kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp