An gudanar da bikin bude taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa dangane da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya karo na 3 a ranar 18 ga wata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda wakilai daga kasashe fiye da 140 da hukumomin kasa da kasa fiye da 30 suka halarta.
A yayin bikin, Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabi, inda ya yi karin haske kan manyan sakamakon raya shawarar cikin shekaru 10 da suka wuce, da takaita kyawawan fasahohin raya shawarar ta hanyar yin tattaunawa tare don cin gajiya da samun nasara tare, da kuma tsara taswirar shirin raya shawarar mai inganci. Ya kuma sanar da matakai da dama da kasar Sin za ta dauka. (Tasallah Yuan)