An gudanar da liyafar murnar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Faransa a babban dakin wasan kwaikwayo na kasar Sin yau Alhamis, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 60 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa, ta samar da moriya ga al’ummomin kasashen biyu, tare da ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban duniya.
Xi ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninsu don tinkarar rashin tabbas da duniya ke fama da shi, tare da daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa. Ya kamata a yi amfani da damar shekarar raya al’adu da yawon shakatawa a tsakanin kasashen biyu da gasar wasannin Olympics ta birnin Paris, a matsayin damammaki na kara yin mu’amala da sada zumunta da juna. Kana ya kamata bangarorin biyu su yi kira ga martaba ra’ayin raya bangarori da dama na duniya da raya tattalin arzikin duniya cikin adalci, da ci gaba da samar da gudummawar Sin da Faransa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tinkarar kalubalen duniya, da kara yin hadin gwiwa da more damar samun ci gaba tare.
A nasa bangare, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron shi ma ya yi jawabi ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, Faransa tana son yin aiki tare da kasar Sin wajen tinkarar kalubalen duniya da daidaita rikice-rikicen kasa da kasa tare. Shekarar 2024, shekara ce ta raya al’adu da yawon shakatawa a tsakanin Faransa da Sin, ya kamat a yi amfani da wannan dama wajen kara yin mu’amala a tsakanin jama’ar kasashen biyu musamman matasa don aza tubalin samun kyakkyawar makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)