A yammacin ranar 4 zuwa safiyar ranar 5 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Xiaogan, da birnin Xianning dake lardin Hubei, inda ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na garin Yunmeng, da wurin shuka kayan lambu na garin Panjiawan dake gundumar Jiayu, da kuma kauyen Siyi, don ganewa idanunsa yadda aka ba da kariya ga kayan tarihi da yin nazarinsu da kuma sa kaimi ga farfado da kauyuka da sauransu.
An ce, gidan adana kayan tarihi na garin Yunmeng, gidan adana kayan tarihi ne na musamman a lardin Hubei, wanda ya kasance gidan adana kayan tarihi na kasar Sin a ma’auni na biyu, wanda ya mallaki kayayyakin tarihi fiye da dubu 5.
Sana’ar shuka kayan lambu, sana’a ce mai muhimmanci kuma ta musamman a garin Panjiawan. Tsawon wurin shuka kayan lambu na garin Panjiawan ya kai kilomita 10, kuma fadinsa ya kai muraba’in kilomita 18, wanda ya hada da kauyukan Panjiawan, da Xiaojiazhou, da Siyi da sauransu, nauyin kayan lambu da aka girba a kowace shekara a wurin ya kai ton dubu 210, ta hakan an sa kaimi ga shuka kayan lambu a gonakin da fadinsu ya kai muraba’in kilomita 66.67 dake garin Panjiawan. (Zainab Zhang)