Jiya Talata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a lardin Qinghai. Ya kai ziyarar a makarantar midil ta Xining dake jihar Guoluo mai cin gashin kanta ta kabilar Zang da haikalin Hongjue, don fahimtar yadda ake gaggauta hadin gwiwar yankin gabas da na yamma wajen ingiza sha’anin ba da ilmi da ba da taimako a wurin, da inganta tunanin ’yan uwan al’ummar kasar Sin na bai daya da habaka kyakkyawar tunanin yayata ruhin kishin kasa tsakanin mabiyan Budha mai asalin yankin Xizang (wato Tibet), har ma da yanayin ciyar da dunkulewar al’ummar Sin gaba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp