Da yammacin jiya Laraba ne babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi rangadin aiki a birnin Shenyang, fadar mulkin lardin Liaoning dake yankin arewa maso gabashin kasar Sin, inda ya ziyarci kamfanin kera na’urar mutum mutumi na Xinsong, da unguwar Mudan ta titin Santaizi, domin ganewa idanun sa yadda ake ingiza kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da kara karfafa gina kungiyoyin JKS, da kyautata aikin samar da hidima a unguwar da sauransu.
Kamfanin Xinsong, kamfani ne dake kera na’urorin zamani, wadanda ake fitar da su zuwa kasashe da yankuna sama da 40 a fadin duniya, kamfanin shi ma yana samar da hidimar kyautata na’urori ga manyan kamfanonin kasa da kasa fiye da 4000.
Yayin ziyararsa a unguwar Mudan, Xi ya jaddada cewa, gyara tsoffin unguwanni, muhimmin aiki ne ga gwamnatin kasar Sin, yayin da take kokarin kyautata rayuwar al’umma. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)