A safiyar yau Alhamis ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar zartaswa ta Turai Charles Michel a babban dakin taruwar jama’a da ke birnin Beijing.
Xi Jinping ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai ta dade da ci gaba, wadda ta dace da muradun bangarorin biyu da na kasashen duniya. Game da ci gaban dangantakar, Xi ya gabatar da ra’ayoyi guda hudu, na farko shi ne tabbatar da sanin juna yadda ya kamata, na biyu shi ne warware sabane-sabane yadda ya kamata, na uku shi ne inganta hadin kansu, sai na hudu kyautata daidaituwa a tsakanin kasa da kasa.
A jawabinsa Michel ya nuna cewa, Tarayyar Turai tana fatan zama abokiyar hadin gwiwar Sin ta kwarai.
A yayin tattaunawar bangarorin biyu kan matsalar Ukraine, Xi ya bayyana matsayin kasar Sin, yana mai cewa, warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa na dacewa da moriyar kasashen Asiya da Turai.
Sannan a wajen taron manema labarai da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta shirya a yau Alhamis, yayin da take amsa tambayar da ta shafi hadin-gwiwar Sin da Turai a fannin tattalin arziki da kasuwanci, mai magana da yawun ma’aikatar Shu Jueting ta bayyana cewa, kasarta na maida hankali sosai wajen bunkasa alakarta da kasashen Turai, da dukufa kan zurfafa hadin-gwiwarsu ta cimma moriyar juna, a wani kokari na tabbatar da samar da isassun kayayyaki a duniya, da kiyaye zaman doka da oda ta fuskar tattalin arziki da kasuwancin kasa da kasa.
Rahotannin sun ce, a karkashin jagorancin shugabannin bangarorin biyu, akwai alakar tattalin arziki mai karfi tsakanin Sin da Turai a halin yanzu. Daga watan Janairu zuwa Oktobar bana, jimillar kudin cinikayyar su ta kai dala biliyan 711.4, adadin da ya karu da kaso 6.3 bisa dari. Kasar Sin ita ce babbar abokiyar cinikayya ta farko ga kungiyar tarayyar Turai wato EU, yayin da EU din ke ci gaba da zama babbar aminiyar cinikayya ta biyu ga kasar ta Sin. (Safiyah Ma, Murtala Zhang)