Bisa gayyatar da shugaba Vladimir Putin na Tarayyar Rasha ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Rasha daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Maris.
Wannan ita ce ziyara ta farko da Xi Jinping ya kai zuwa ketare tun bayan da aka sake zabar sa a matsayin shugaban kasar, kuma ziyara ce ta sada zumunci da tabbatar da hadin gwiwa da zaman lafiya, kana hanyar da za ta jagoranta da kuma tsara tsari kan dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani.
Xi Jinping ya taba bayyana dangantakarsa da Putin a matsayin “alakar ra’ayin bai daya” kuma “ta aminci”. Shi ma a nasa bangaren shugaba Putin ya kira Xi Jinping “aboki nagari” kuma “aboki na aminci”. A watan Maris din shekarar 2013, lokacin da Xi Jinping, ya hau karagar mulkin kasar Sin karo na farko, ya zabi kasar Rasha a matsayin kasar da zai kai ziyararsa ta farko a kasashen waje.
Duk wani irin ci gaba da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, kan dangantakar Sin da Rasha, ba za ta rasa nasaba da jagorancin shugabannin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ba. A cikin wadannan shekaru goma kuma, Xi Jinping da Putin sun yi ganawa har sau 40. A karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, Sin da Rasha sun yi nasarar shimfida hanyar amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin manyan kasashen duniya, da yin mu’amalar sada zumunta tsakanin kasashen da ke makwabtaka, lamarin da ya zama abin koyi ga karfafa huldar kasa da kasa.
Wannan ziyarar da Xi Jinping zai kai kasar Rasha, shi ne karo na 9 da ya taka kafarsa a kasar Rasha tun bayan da ya hau kan karagar mulki. A kwanan baya, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, a yayin wannan ziyara, Xi Jinping da Putin za su yi musayar ra’ayi mai zurfi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu duka, kana da sa kaimi ga yin hakikanin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da kuma kaddamar da sabon kuzari ga ci gaban dangantakar kasashen biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)