A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin.
An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp