Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya fada a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kwamitin wasannin Olympic na duniya watau IOC, domin ci gaba da bunkasa wasannin na Olympic.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kwamitin na IOC, Thomas Bach a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Bach ya tafi yankin ne domin bikin bude gasar wasannin lokacin hunturu ta Asiya karo na 9.
- Aikin Gina Babbar Mayankar Dabbobi Zai Taimaka Wajen Kara Samar Da Wadataccen Nama A Nijeriya – Minista
- Rashin Aiwatar Da Sabon Tsarin Ilimi Na Kasa Na Kawo Cikas Ga Bunkasar Ilimi A Nijeriya
Shugaba Xi ya bayyana cewa, nasarar da kasar Sin ta samu wajen karbar bakuncin manyan wasannin motsa jiki da dama a cikin ‘yan shekarun nan, ta nuna cudanya da hadin gwiwa na kut-da-kut da ke tsakanin Sin da kwamitin IOC.
Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana ci gaba da bunkasa fannin wasanni, da kuma kara kokarin cimma burin gina cibiyar wasannin motsa jiki, da tabbatar da samuwar kasar Sin mai koshin lafiya, wadda za ta ci gaba da ba da sabbin gudummawa ga ci gaban wasannin motsa jiki na duniya.
A nasa bangaren, Bach ya yaba wa kasar Sin bisa ba da shawarwari da aiwatar da manufofin hadin kai, da hadin gwiwa, da daidaito da mutunta juna, da kiyaye ra’ayoyin bangarori daban-daban, da nuna adawa da siyasantar da harkokin wasanni, da ba da goyon baya ga samar da damammaki ga kasashe masu tasowa don shiga a dama da su cikin harkokin wasanni na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)