An samu koma baya wajen aiwatar da sabon tsarin ilim wanda gwamnatin tarayya niyyar fara amfani da shi a watan Janairu 2025, watan ne aka tsaida wanda za a fara amfani da shi sabon tsarin ilimin na kasa.
Gwamnatin tarayya tana da tata manufa wadda ta so ta cimmawa a bangaren sabon tsarin ilimi na kasa, wanda an yi haka ne saboda a samu damar inganta ilim a duk fadin tarayyar Nijeriya.
- Sin Na Rike Matsayinta Na Kasa Mafi Girma Wajen Cinikin Kayayyaki Tsawon Shekaru 8 A Jere
- Farashin Kayan Abinici Ya Karu Da Kashi 91.6 Cikin Shekara Daya -NBS
Shi sabon tsarin a cikin shi an yi niyya ce ta yadda za a rika koyawa ‘yan makaranta yadda za su rika tunanin da zai taimake su wajen gwagwarmayar neman ilimin da suke, ga kuma yadda za a rika koya masu su rika yin abubuwa da hannun su kowa yana ganin yadda aka yi, lamarin d aka so aiwatar da shi a watan Janairu 2025.
Tsohon Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman, shi ne wanda ya bayyana cewa sabon tsarin ilimi na karamar Mkarantar Sakandare za a fa amfani da shi ne watan Janairu 2025.
Domin tabbatar da hakan gwamnatin ta yi shirin fara sa abubuwa kan saiti daga watan Oktoba zuwa Disamba na shekarar 2024,lamarin da ya hada da yadda za a rika koyawa Malami da kuma bunkasar kayan aiki.
Su tsare tsaren anyi shirin tabbatar dukkan makarantu masu zaman kan su da na gwamnati za su fara amfani da tsarin a watan Janairu 2025.
Sai dai kuma watan Janairu ya wuce ba tare da samun wani ci gab aba dangane da lamarin. Rahoto ya nuna har yanzu da akwai sauran Rina a Kaba, domin kuwa da akwai karancin makarantu wadanda basu da irin kayan da za ayiu amfani da su wajen aiwatar da sabon tsarin,da kuma yadda za a horar da Malamai, hakan ta sa aka bar masu ruwa da tsaki cikin shakku ko sabon tsarin ilimin za afara amfani da shi.
Sabon tsarin ilimin an yi niyyar fara amfanni da shi inda za a koyar da yaddaake sabbin sana’oi na hannu 15 na karamar makarantar Firamare da sakandare inda aka yi fatan maida hankali ne kan koyawa dalibai sana’oi daban- daban, tun daga Firamare zuwa Sakandare.Sabbin sana’oin sun hada da yadda za koyi karau ta kafar sadarwa ta zaman IT, gini ta hanyar zamani ta robotics, lamarin da ya shafi aikin hotel,koyon dinki, da kuma lamarin aikin.
Duk kuwa da kwai karuwar da sabon tsarin ilimin yake tafe da ita, binciken da aka yi ta tafiye- tafiye a makarantu masu zaman kansu da kuma na gwamnati a Babban Birnin Tarayya ya nun aba da gaske ake ba lamarin fara amfani da sabon tsarin ilimi na kasa. Makarantu da dama basu shiryawa amfani da sabon tsarin ilimin ba.
Sabon tsarin ilimin an bullo da shi ne domin a samun maganin matsalolin ilim da ake fuskanta a sashen ilimi na kasar Nijeriya, abinda ya hada tsarin koyarwa na shekarun baya da suka wuce, babu abubuwan da za su taimaka wajen koyawa dalibai, da kuma yadda aka yiu wa lamarin rikon sakainar Kashi.
Hakanan ma shit sarin yayi kama da irin wanda ake yi a kasashen da suka ci gaba,inda ake koyawa ‘yan makaranta yadda za a koya masu sana’oin da za su taimaka masu matsayi na dogaro da ka,abubuwan da aka dade ana yi a kasashen duniya.Muhimman abubuwan cikin sabon tsarin ilimin inda aka kara sa wasu sabbin abubuwa a wasu darussa kamar Lissafi, kimiyya, da kuma abind a mutum zai iya koya da hannun sa, har ma da maida hankali akan fasaha a cikin azuzuwa.
Gwamnati ta yi alkawarin za ta bada duk taimakon da ya kamata domin a tabbatar da cewa an samu fara aiki da sabon tsarin ilimi, sai dai kuma su alkawuran sun ba haka aka yi tsammanin lamarinzi kasance ba, kowa lamarin ya ba shi mamaki.
Irin wannan abin ya sa mutane da damar ansu ya baci kuma abin ya basu kunya daga cikin wadanda suke da ruwa da tsaki,wadanda suke ganin koma baya irin hakan, yana kara taazzara lamarin ne na matsalolin ilimi ne da ‘yan Nijeriya suka dade da fuskanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp