Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa kasarsa ta shirya tsaf domin yin aiki tare da kasar Peru wajen samun nasarar hadin gwiwar mabambantan kasashen duniya da inganta hanyoyin samun daidaito da kwanciyar hankali a duniya da kuma tattalin arziki mai gamewa da zai amfanar da kowa da kowa a tsakanin kasashen.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne a mukalar da ya rubuta, wadda aka wallafa a yau Alhamis, a wata kafar yada labarai ta kasar Peru mai suna El Peruano.
Mukalar mai taken Kawancen Kasar Sin da Peru: Kokarin Samun Rayuwar Gaba Mai Albarka, an fitar da ita ce a yayin da Xi ke kan hanyarsa ta zuwa Peru domin taron kwarya kwarya karo na 31 na shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arziki ta yankin Asiya da tekun Fasifik wato APEC, a birnin Lima da kuma ziyarar aiki da zai kai kasar dake yankin Latin Amurka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)