A yau Alhamis 10 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron koli na kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean (CELAC), karo na 9 wanda aka bude a jiya Laraba a Tegucigalpa, babban birnin kasar Honduras.
A cikin sakon taya murnar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a yau duniya tana samun sauye-sauye cikin hanzari wanda ba a taba ganin irinsu ba a tsawon karni guda, kuma kasashe masu tasowa, ciki har da Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, suna samun bunkasa mai matukar kuzari.
Ya kara da cewa, CELAC ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da ‘yancin kai, da dogaro da kai, da kara karfi ta hanyar hadin kai, tare da taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da habaka ci gaba, da inganta hadin gwiwa, da kuma zurfafa dinkewar yankin.
Shugaban na kasar Sin ya kuma yi fatan alheri ga kasashe da jama’ar yankin na Latin Amurka da Caribbean wajen samun manyan nasarori a fannin ci gaba, da farfado da tattalin arziki, ta yadda za su ba da gagarumar gudummawa ga hadin kai da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp