A ranar Asabar da ta gabata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Brice Clotaire Oligui Nguema kan zabarsa da aka yi a matsayin shugaban kasar jamhuriyar Gabon.
A cikin sakon nasa, Xi ya bayyana cewa, kasashen Sin da Gabon suna da dadadden zumunci, yana mai cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, an kara zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, kuma hadin gwiwa a fannoni daban daban ya haifar da kyawawan sakamako. Ya kara da cewa, kasashen biyu sun tabbatar da goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi muhimman muradun juna. Kazalika, yana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Gabon, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da zababben shugaban kasar Nguema, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a nan birnin Beijing, a matsayin wata dama ta sa kaimi ga tabbatar da ci gaba mai dorewa na hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, ta yadda jama’arsu za su amfana.
A wannan rana har ila yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Daniel Noboa bisa sake zabarsa da aka yi a matsayin shugaban kasar Ecuador. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp